Indonesia

An Yi Addu'oi Na Musamman A Indonesia Don Mamata Kusan 1,600

Yadda girgizan kasa ta yi barna a Indonesia
Yadda girgizan kasa ta yi barna a Indonesia rfi

Al'ummar kasar Indonesia sun yi addu'oi na musamman don rokon Allah ya gafartawa mamata  sakamakon if'tilain girgizan kasa da aka samu a tsubirin Sulawesi inda alkaluman mamata ke nuna sun doshi 1,600.

Talla

Jimil'lan gidaje dubu sabain suka rushe yayinda har yanzu akwai wasu mutane akalla dubu daya da babu wanda ya san inda suka makale.

Ma'aikatar lafiya ta kasar ta fadi cewa an tura jami'an lafiya 855 domin kai dauki yankin don fargaban bullar wasu cutuka daka iya  barkewa.

A yanzu haka kasashen duniya da kungiyoyi na ta aikewa da taimako zuwa Indonesia mako baya bayan aukuwar girgizan kasa da ambaliyar ruwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.