Afrika- Amurka

Matar Donald Trump Ta Kammala Ziyara A Afrika

Uwargida Melania Trumptana wasa da wani karamin giwa yayin ziyara a Nairobi na Kenya ranar 5 Oktoba 2018
Uwargida Melania Trumptana wasa da wani karamin giwa yayin ziyara a Nairobi na Kenya ranar 5 Oktoba 2018 rfi

Uwargidan shugaban Amurka Melania Trump na karkare ziyara kasashe hudu na Africa yau lahadi da ziyara kasar Masar.

Talla

A wani tsokaci da yayi mijin nata Donald Trump ya shaidawa manema labarai cewa matarsa na ziyara kasashen Afrika ne don ta nuna sun damu da jama’a.

Ziyarar Uwargida Melania Trump ya kai ta zuwa kasashen  Ghana, Malawi, Kenya sai kuma Masar.

A lokacinda aka tambaye ta yadda take kallon kalaman mijinta a wani lokaci a baya inda yake cewa ‘yan Africa da ‘yan kasar Haiti tamkar wajen kashi yake kallon su, Melania Trump ta ce ita dai bata ji maigidanta ya taba fadin haka ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.