Isa ga babban shafi
Francophonie-Rwanda

An zabi ministan wajen Rwanda uwargida Louise Mushikiwabo shugabar Francophonie

Louise Mushikiwabo, minista harakokin wajen Rwanda
Louise Mushikiwabo, minista harakokin wajen Rwanda Ludovic MARIN / AFP
Zubin rubutu: Salissou Hamissou
2 Minti

Zaben da aka yiwa Louise Mushikiwabo domin shugabantar kungiyar Francophonie, a yau juma’a wani gagarumin ci gaba ne ga diflomasiyar kasar Rwanda, da ke tabbatar da kokarin da kasar ke ta yi a yan shekarun da suka gabata wajen kara tabbatar da matsayinta a Afrika da ma duniya baki daya.

Talla

Ministar harakokin wajen kasar ta Rwanda mai shekaru 57 a duniya ce aka zaba ta shugabancin kungiyar ta Francophonie (OIF) a gaban abiokiyar takararta shugabar kungiyar mai barin gado yar kasar Canada Michaëlle Jean, duk da sukar kasar ta ke sha wajen kin mutunta hakkin dan adam

Uwargida Mushikiwabo, da ta ziyarci kasashe da dama domin kare manufofinta da kuma haibar kasarta Rwanda, ta samu goyon bayan kasashen Afrika da kuma Fransa ne.

Zaben ta kan wannan mukami wata gagarumar nasara ce ga shugaban Rwanda Paul Kagame, da ya tilsata zabinsa ga takwarorinsa na Afrika, da ma shugaba Emmanuel Macron na Faransa, dake fatan samun kusanci da yar karamar kasar dake yankin babban tafkin gabashin Afrika

Za a iya cewa takarar uwargida Mushikiwabo ta zo wa kungiyar ta Francophonie a ba zata, Ganin a baya kasar Rwanda ta bayyana aniyarta ta nisantar Faransa da ya sa a 2008 kasar ta musaya faransanci da Igilishi a matsayin harshen koyarwa a makarantu bako, tare da shiga kungiyar Commonwealth a 2009.

Wannan dai na zuwa ne duk kuwa da tsamin dangantakar dake tsakanin Rwanda da Faransa sakamakon zargin da gwamnatin Kigali ta yi wa Faransa da taka muhimiyar rawa a cikin kisan kare dangin 1994 da yayi sanadiyar mutuwar mutane dubu (800.000), duk kuwa da sake maida huldar da suka yi a 2009.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.