Saudiya

Kamfanonin duniya sun kaurace wa taron Saudiya

Jamal Khashoggi da ake zargin Saudiya da kashe shi
Jamal Khashoggi da ake zargin Saudiya da kashe shi MOHAMMED AL-SHAIKH / AFP

Kamfanoni da sauran cibiyoyi masu zaman kansu, sun bayyana aniyarsu ta kaurace wa taron tattalin arziki da saka jari wanda ya kamata a gudanar cikin makon gobe a birnin Riyad na kasar Saudiyya, sakamakon zargin da ake yi wa mahukuntan kasar na kashe dan Jaridar Jamal Khashoggi a birnin Santanbul na Turkiyya.

Talla

Daga cikin shahararrun cibiyoyi da kuma kamfanonin hada-hadar kudade da suka sanar da aniyarsu ta kaurace wa wannan taro sun hada Bloomberg, da Financial Times da kuma jaridar New York Times da ke Amurka.

Har ila yau Richard Branson, shugaban kamfanin Virgin, ya sanar da dakatar da duk wasu harkokin kasuwaci tsakanin kamfanin da Saudiyya, sannan ya ce, ba za su aike da wakili zuwa taron na makon gobe ba.

Karin manyan kamfanonin da suka bayyana kaurace wa taron, sun hada da Ford da ke kera motoci, sai kuma Google da ya shahara a fannin sadarwa da kuma UBER da ke harkar sufuri, yayin da a Turai bankuna suka bi sahunsu, da suka hada da HBSC da BNP Paribas da kuma JP Morgan.

Shugaban Bankin Duniya Jim Yong Kim da Christine La Garde ta IMF duk sun ce, ba za su halarci taron ba saboda bacewar Jamal Khashoggi da ake zargin Saudiya da kashe shi har lahira.

Kazalika shugabannin kamfanin Master Card da na Bankin Societe Generale da Standard Chartered da kuma shugaban kasuwar hannayen jari ta London duk sun ce, ba za su halarci taron ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.