Amurka-Rasha

Amurka na ganawa da Rasha bayan karya yarjejeniyar nukiliya

Mashawarcin shugaban Amurka kan harkokin tsaro,  John Bolton
Mashawarcin shugaban Amurka kan harkokin tsaro, John Bolton REUTERS/Denis Balibouse

Mai bai wa shugaban Amurka shawara a fannin tsaro, John Bolton a ya fara wata ziyarar kwanaki biyu a birnin Moscow don ganawa da jami’an Rasha biyo bayan sanarwar da shugaba Donald Trump ya yi ta janyewar Amurka daga yarjejeniyar makaman nukiliya da aka yi tun zamanin yakin cacar-baka.

Talla

Wannan ziyarar ta Bolton, an shiryata ne tun kafin sanarwar da shugaba Donald Trump ya yi ta janyewa daga yarjejniyar da ta kai shekaru 30, matakin da Rasha ta bayyana a matsayin mai hatsari.

A shekara ta 1987 ne aka kulla yarjejeniyar a zamanin shugaban Amurka Ronald Reagan, da kuma Shugaban Tsohuwar Tarayyar Soviet na karshe, Mikhail Gorbachev, wanda a ranar Lahadi ya soki matakin na Trump, yana mai bayyana shi da mai hatsari kuma babu hikima a cikinsa.

Fadar shugaban Rasha ta Kremlim ta ce, ana kyautata zaton a ranar Talata Bolton zai tattauna da shugaba Putin, wanda ke neman karin haske kan matakin Amurka.

Bolton wanda ya sauka kasar ta gabashin Turai a ranar Lahadi, zai kuma gana da Ministan Harkokin Wajen Rasha, Sergei Lavrov.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya kira shugaba Trump ta wayar tarho, in da yake jaddada mahimmancin daddadiyar yarjejeniyar.

Kazalika, Majalisar Tarayyar Turai ta bukaci Amurka da Rasha da su zauna don sake duba wannan batu, tana mai nuni da cewa wannan yarjejeniyar ta takaita makaman nukiliya masu cin matsakaicin zango.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI