Saudiya-Turkiya

Ana dakon Turkiya ta fasa kwai kan mutuwar Khashoggi

Jamal Khashoggi
Jamal Khashoggi AFP/Mohammed Al-Shaikh

Mahukunta a Turkiyya za su fitar da sakamakon nasu bincike dangane da hakikanin gaskiyar abin da ya faru da dan jarida Jamal Khashoggi wanda ya mutu a ofishin jakadancin Saudiyya da ke birnin Santanbul.

Talla

Bayan da suka dauki dogon lokaci suna inkarin cewa ba su da masaniya a game da makomarsa, daga bisani dai mahukuntan kasar ta Saudiyya sun tabbatar da mutuwar Khashoggi mai shekaru 59 a cikin ofishin jakadancinta, to sai dai Turkiyya ta ce, a yau talata ne za ta bayyana yadda aka kashe wannan dan jaridar mai sukar lamirin gidan sarautar Saudiyya.

A bangare guda, Saudiya ta bude babban taron zuba hannayen jari a birnin Riyad duk da cewa, kasashe da dama da suka hada da ‘yan kasuwa da manyan kamfanoni da bankuna sun kaurace wa taron sakamakon dambarwar kisan Khashoggi.

An tanadi matakan tsaro mai tsauri a wannan taro da ke gudana a Otel din Ritz-Carlton kuma kamar yadda rahotanni ke tabbatarwa, daga cikin masu gabatar da makala har da shugaban asusun zuba hannayen jarin-kai tsaye na Rasha, Kirill Dmitriyev da shugaban Kamfanin Makamashi na Total da ke Faransa, Patrick Pouyanne da kuma Firaministan Pakistan, Imran Khan

Shugabar Asusun bada Lamuni na Duniya, Christine Lagarde da Sakataren Baitil Malin Amurka, Steven Mnuchin duk sun kaurace wa gagarumin taron da ya samu nakasu sakamakon kisan Khashoggi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.