Amurka-Democrat

Sakon abubuwa masu fashewa sun isa ga muhimman mutane a Amurka

Ana dai dakon jawaban shugaba Donald Trump kowanne lokaci daga yanzu.
Ana dai dakon jawaban shugaba Donald Trump kowanne lokaci daga yanzu. ©REUTERS/Jonathan Ernst

Hukumomin tsaro a Amurka sun tabbatar da isar wasu sakonnin abubuwa masu fashewa da ake kyautata zaton bom ne zuwa gidajen jiga-jigan jam'iyyar Democrat da tsakar ranar yau Laraba.

Talla

Rahotanni sun ce sakonnin sun isa gidan tsohon shugaban kasar Barrack Obama da Hillary Clinton Ofishin jarida na CNN da gidan gwamnan birnin Newyork dama tsohon Atoni Janar na kasar.

Tuni hukumar tsaro ta FBI ta bazama gidajen da suka samu wannan sako tare da kwararru a fannin kwance bom.

Kawo yanzu dai ba a tabbatar da cewa abubuwan masu fashewa ba ne yayinda ake jiran jawabin shugaba Donald Trump kowanne lokaci daga yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.