Honduras-Amurka

'Yan ciranin Honduras na ci gaba da tattaki zuwa Amurka a kafa

Ayarin ‘yan cirani daga kasar Honduras masu kalubalantar Donald Trump ta hanyar takawa a kafa don shiga Amurka ciki har da daruruwan yara wadanda iyayensu suka yi imanin daukan kowacce kasada don ganin sun basu ingantacciyar rayuwa, yanzu haka na ci gaba da tsallaka iyakar ruwa cikin tarin turmutsutsu don Isa ga Amurkan duk kuwa da matakan shugaban kasar Donald Trump.

Cikin mutane fiye da dubu 7 da ke tattakin yanzu haka zuwa Amurka, Majalisar Dinkin Duniya ta ce kashi 1 bisa ukunsu kankanan yara ne sai kuma tarin mata da suka mamaye ayarin.
Cikin mutane fiye da dubu 7 da ke tattakin yanzu haka zuwa Amurka, Majalisar Dinkin Duniya ta ce kashi 1 bisa ukunsu kankanan yara ne sai kuma tarin mata da suka mamaye ayarin. REUTERS/Jorge Cabrera
Talla

Cikin kwanaki 5 da suka gabata bayan da dubban ‘yan ciranin suka samu shiga Mexico daga Guatemala iyaye da dama sun rika sakin ‘ya’yayensu don su samu damar shiga turmutsutsun masu tsallakawa Amurka ta ruwa.

A cewar iyayen wadanda suka yi imanin daukar kowacce kasada don ganin ‘ya’yansu sun samu tsallakawa Amurka da nufin samun ingantacciyar rayuwa, basu da zabin da wuce hakan la’akari da irin tsananin talauci baya ga rikicin da ya korosu daga Honduras.

Galibin iyaye mata da ke cikin ayarin ‘yan ciranin sun bar Honduras ne don kare ‘ya’yayensu daga hare-haren ‘yan daba da suka yi kaurin suna wajen ko dai kashe yaran ko daukarsu aiki bisa tilasci ko kuma yiwa matan cikinsu Fyade baya ga tsananin talaucin da kasar ta fada.

Cikin tafiyar ta su da ke cike da hadari zuwa Iyakar Mexico tarin iyaye ne suka sadaukar da rayukansu ta hanyar zura ‘ya’yayensu nasu ta sarkakakkiyar hanyar da Mexico ta toshe don su samu isa cikin kasar su kuma tasamma Amurka.

Cikin mutane fiye da dubu 7 da ke tattakin yanzu haka zuwa Amurka, Majalisar Dinkin Duniya ta ce kashi 1 bisa ukunsu kankanan yara ne sai kuma tarin mata da suka mamaye ayarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI