Amurka

Jami'an tsaron Amurka na bincike kan wanda da ya aika wasikun bam

Kawo yanzu dai babu cikakken bayani kan wadanda ke da hannu wajen daukar nauyin aikewa da sakonnin bama-baman.
Kawo yanzu dai babu cikakken bayani kan wadanda ke da hannu wajen daukar nauyin aikewa da sakonnin bama-baman. REUTERS/Mike Segar

Jami’an tsaron Amurka na ci gaba da bincike kan Cesar Altieri Sayoc, mutumin da suka kama a jiya Juma’a bisa zargin shi ne ya aike da wasiku akalla 13 makale da bama-bamai zuwa ga wasu manyan masu adawa da shugaba Donald Trump, ciki harda Hillary Clinton.

Talla

Jami’an tsaro sun gano wata mota da Sayoc mai shekaru 56 ya manne da hotunan shugaba Trump, hade da mamaye shafukansa na sadarwar zamani da rubuce-rubuce da hotunan shugaban, abinda ke bayyana shi a matsayin mai zazzafan ra’ayin goyon bayan shugaba Donald Trump.

Bincike ya nuna cewa, an sha kama wanda ake zargin bisa aikata laifuka daban daban a shekarun baya, ciki harda shekarar 2002, inda aka kama shi bisa laifin yin barazanar, danawa wani kamfanin samar da makamashi bam, zalika an taba kama shi da laifukan sata da kuma cin zarafin dan adam.

Kamen na zuwa a dai dai lokacin da aka yi nasarar kwance bom na 10 cikin sakwannin bama-bamai 12 da aka aikewa masu adawa da shugaban kasar.

Bayanai na cewa dukkan wadannan sunki-sunki na bama-bamai sun iso ne cikin ambulan da kan sarki mai dauke da tutar Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.