Amurka

Masu bincike na kokarin tanttance sakwannin bama-bamai

Tsohon Shugaba Barack Obama da tsohon mataimakin sa Joe Biden,
Tsohon Shugaba Barack Obama da tsohon mataimakin sa Joe Biden, REUTERS/Carlos Barria

Tsohon mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden da wani shahrarren mai gudanar da fim Robert De Niro su ne na baya-bayan nan da aka aike wa sakwannin takarda da masana suka bayyana su da cewa bama-bamai ne.

Talla

Mafi yawan wadanda aka aikewa irin wadannan sakwanni na daga cikin masu sukar salon siyasar shugaba Donald Trump ne, to sai dai a cikin daren da ya gabata jami’an hukumar FBI sun cigaba da bincike domin gano wadanda ke da hannu wajen aikewa da wadannan sakwanni a dai dai lokacin da Amurka ke shirin zuwa zaben rabin tsakiyar wa’adin shugabanci.

Masu bincike sun soma gano daga yankin da aka aiko da wadanan sakwanni a cewar wani jami`in tsaro zuwa ga manema labarai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.