Amurka

Shugaba Trump zai aikewa da dakaru kan iyaka da Mexico

Yan kasar Mexico saman hanyar su ta zuwa Amurka
Yan kasar Mexico saman hanyar su ta zuwa Amurka ©REUTERS/Ueslei Marcelino

Ma`aikatar tsaro na Amurka na shirin aikewa da dakaru kusan 800 zuwa kan iyakan kasar da Mexico, biyo bayan shelan da Shugaba Donald Trump yayi dake cewa za’a yi amfani da dakarun don ayyukan kare kasa.

Talla

Dakaru 800 zasu marawa wasu sojoji dubu 2 da tuni aka tura kan iyakar, wadanda aka dibo su daga rundunoni daban-daban na sojan Amurka.

Sakataren tsaron Amurka Jim Mattis ake sa ran ya bada umarni,

Zuwa ayarin dakarun da zasu tafi kan iyakan kasar da Mexico, zasu kunshi likitoci da injiniyoyi da zasu kula da kafa bukkoki wato tanttuna, da kula da sufuri da sauran kayan aiki.

Tun jiya Alhamis Shugaban Amurkan Donald Trump ke cewa tsarin tsohuwar gwamnatin daya gada na haifar masa da cikas a kokarinsa na tabbatar da tsaron kan iyakokin kasar.

Matakin Trump yanzu haka na zuwa ne a wani lokaci da wasu dubban bakin haure cikin mota daga wani gari na Mexico ke kokarin kutsa kai cikin Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.