Brazil

Bolsonaro ya lashe zaben shugaban kasar Brazil

Zababben Shugaban Brazil Jair Bolsonaro
Zababben Shugaban Brazil Jair Bolsonaro REUTERS/Pilar Olivares

Tsohon kaften din sojin Brazil mai ra’ayin rikau, Jair Bolsonaro ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a karshen mako, in da ya doke abokin takararsa Fernando Haddad da sama da kashi 55 na kuri’un da aka kada.

Talla

Jim kadan da samun nasarar Mr. Bolsonaro a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar, magoya bayansa suka fantsama kan tituna musamman a birnin Rio de Janeiro, in da suka gudanar da wasan wuta tare da daga tutar Brazil sama.

Sakamakon zaben ya nuna cewa, Bolsonaro ya samu kashi 55.18 na kuri’un da aka kada, yayin da ya lashi takobin ceto Brazil daga tarin matsalolin da ke addabar ta da suka hada da cin hanci da rashawa har ma da tabarbarewar tattalin arziki.

Bolsonaro wanda ya kasance tsohon dan majalisa, ya kuma yi alkawarin kare kundin tsarin mulkin kasar da demokradiya da kuma ‘yan cin walwala, abin da ke nuna cewa, ya yi watsi da ikirarin ‘yan adawa da ke cewa, zai gudanar da mulkin kama karya a kasar, ganin yadda ya fito karara ya bayyana goyon bayansa ga azabtarwar da sojoji suka yi wa al’umma a lokacin mulkinsu tsakanin 1964-1985.

Ana saran zababben shugaban mai shekaru 63 ya sha rantsuwar kama aiki a ranar 1 ga watan Janairu mai zuwa, yayin da bayanai ke cewa, kawo yanzu abokin takararsa, Haddad bai kira sa ta wayar tarho don taya shi murna ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.