Indonesia

Jirgin sama dauke da mutane 189 ya yi hatsari

Ana fargabar mutuwar daukacin mutanen da ke cikin jirgin Lion Air da ya yi hatsari a tekn Java
Ana fargabar mutuwar daukacin mutanen da ke cikin jirgin Lion Air da ya yi hatsari a tekn Java Flightradar24/twitter.com

Jirgin saman Indonesia na Lion Air ya yi hatsari a teku dauke da mutane 189 da suka hada da fasinjoji da ma’aikata har ma da kananan yara.

Talla

Jirgin kirar Boeing 737 MAX da bai dade da fara aiki ba, ya bace ne bayan minti 13 da tashinsa daga filin jiragen sama da ke babban birnin kasar, in da ya sulmiya cikin tekun Java.

Jami’an agaji na ci gaba da kokarin neman jirgin da ya nufi birnin Pangkal Pinang daga Jakarta, yayin da bayanai ke cewa, nutsewarsa ta kai mita 30-40 a cikin tekun.

Hukumar Kula da Sufuri ta Indonesia ta ce, akwai yaro guda da jarirai guda biyu a cikin wadanda ibtila'in hatsarin ya rutsa da su da misalin karfe 6:30 na safe agogon kasar.

Ma’aiktar Kudi ta Indonesia ta tabbatar cewa, akwai ma’aikatanta kimanin 20 a cikin wannan jirgin na Lion Air.

A wannan shekara ta 2018 aka kera jirgin kuma a ranar 15 ga watan Aguta ya fara aiki a kamfanin na Lion Air.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.