Rashin hukunta masu kashe 'yan jarida babban kalubale ne - CPJ

(17/02/2016) Wasu 'yan jaridu a kasar India yayin zanga-zanga dangane da cin zarafin 'yan jaridu.
(17/02/2016) Wasu 'yan jaridu a kasar India yayin zanga-zanga dangane da cin zarafin 'yan jaridu. Indranil Mukherjee/AFP/Getty Images

Kungiyar dake kare hakkokin Yan jaridu ta duniya at CPJ tace rashin hukunta masu kashe Yan Jaridu na bada dama wajen yiwa aikin jaridar karan tsaye.

Talla

Rahotan karo na 11 da kungiyar ke fitarwa kowacce shekara ya bayyana jerin sunayen kasashen da ake yawan kasha Yan Jaridu akai akai, yayin da ba’a hukunta makasan.

Kasashen 14 da sunayen su ya fito cikin rahotan sun dade suna bayyana kan wanan aika aika tun daga shekarar 2008 da aka fara wallafa rahotan.

Elisabeth Witchel, jami’ar da ta wallafa rahotan ta bayyana Somalia a matsayin kasa ta farko, sai kuma Afghansitan, Colombia da kuma Ecuador.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.