Indonesia

An gano bakin akwatin jirgin Indonesia da ya hatsari a teku

Ana ci gaba da neman bakin akwati na biyu na jirgin Lion Air da ya yi hatsari a tekun Java
Ana ci gaba da neman bakin akwati na biyu na jirgin Lion Air da ya yi hatsari a tekun Java Antara Foto/Handout/Basarnas via REUTERS

Gwanayen ninkaya sun yi nasarar gano bakin akwatin jirgin Lion Air da ya yi hatsari a tekun Indonesia dauke da fasinjoji 189.

Talla

Jirgin ya fada tekun Java ne jim kadan da tashinsa daga babban birnin Jakarta a ranar Litinin, kuma babu ko da fasinja guda da aka gano da rai.

Kawo yanzu babu wata alama da ke nuni da musabbabin hadarin sabon jirgin, amma wasu rahotanni na cewa, ya gamu da wata matsala a jajibirin ranar hatsarin.

Masu ninkayar sun ce, sun gano bakin akwatin ne a can kasan tekun kuma a karkashin baraguzan jirgin, koda yake ana ci gaba da neman bakin awkati na biyu da ya nadi hirar matuka jirgin gabanin aukuwar ibtila’in.

Na’urar bakin akwati na taka muhimmiyar rawa da kusan kashi 90 wajen bayar da bayanai game da hadduran jiragen sama a duniya kamar yadda kwararru a fannin zirga-zirgar jiragen suka ce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.