Amurka

Maharin Pittsburg a Amurka zai gurfana gaban Kotu

Matakin gurafanar da Bowers gaban Kotu na zuwa a dai dai lokacin da iyalan wadanda harin ya rutsa da su ke ci gaba da makoki.
Matakin gurafanar da Bowers gaban Kotu na zuwa a dai dai lokacin da iyalan wadanda harin ya rutsa da su ke ci gaba da makoki. ©REUTERS/Kevin Lamarque

Maharin Pittsburgh a Amurka da ya kai farmaki kan mabiya addinin yahudu Robert Bowers zai gurfana gaban kotu yau Alhamis don amsa tuhuma kan harin bindigar da ya hallaka tarin jama’a baya ga jikkata wasu da dama.

Talla

Matakin gurfanar da Mr Robert Bowers maharin na Pittsburg cikin karshen makon jiya, na zuwa ne a dai dai lokacin da iyalan wadanda harin ya rutsa da su ke ci gaba da zaman makoki yayinda a bangare guda al'umma ke ci gaba da neman lallai a hukunta maharin.

Robert Bowers, mai shekaru 46 wanda ya kai harin bindigar kan mabiya addinin yahudu tare da hallaka wasu 11 baya jikkata da dama zai gurfana gaban kotun kowanne lokaci a yau Alhamis inda Kotun ke tuhumarsa da laifuka 44 ciki har da ayyukan ta’addanci.

Bowers wanda wannan ne karo na biyu da ya ke gurfana gaban Kotu tun bayan harin na Pittsburgh cikin karshen makon jiya, ko a Litinin din da ya gabata ya bayyana gaban kotu tare da amsa wasu tuhume-tuhume.

Maharin wanda ake ci gaba da tsare shi a gidan yarin Butler County cikin tuhume-tuhume 44 da ake da su akansa akalla guda 10 daga ciki idan har ya amsa aikata su babu shakka Kotu za ta yanke masa hukuncin kisa ne.

Yanzu haka dai Robert Bower na ci gaba da karbar kulawar lafiya ne sakamakon raunin da ya samu a kafafuwansa yayin harin na makon jiya wanda hukumomi suka bayyana da na ta’addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.