Isa ga babban shafi
Trump-Obama

Ana ci gaba da yakin neman zaben tsakiyar wa'adi a Amurka

Shi ma dai cikin kalamansa Barrack Obama, ya kafa misali da umarnin gwamnatin Amurkan na harbin ‘yan ciranin Caravan, wadanda ya ce suna kan hanyar su ne saboda sun yi imani da Amurka.
Shi ma dai cikin kalamansa Barrack Obama, ya kafa misali da umarnin gwamnatin Amurkan na harbin ‘yan ciranin Caravan, wadanda ya ce suna kan hanyar su ne saboda sun yi imani da Amurka. REUTERS/Al Drago
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
Minti 2

A dai dai lokacin da ake gab da karkare yakin neman zaben tsakiyar wa’adi can a kasar Amurka tsakanin Jam’iyya mai mulki ta Republican da kuma babbar Jam’iyyar adawa ta Democrat, yanzu haka jam’iyyar adawar na barazana ga karbuwar da shugaba Trump ke ganin ya samu a wajen al’ummar kasar.

Talla

Bayan shafe ‘yan kwanaki ana gudanar da gangamin yakin neman zaben wanda shugaban na Amurka Donald Trump ke alfahari da irin rawar da ya taka wajen farfado da tattalin arzikin kasar, musamman ta fuskar janyewa daga duk wata yarjejeniyar kasuwanci da ya ke ganin ana ci da gumin kasar baya ga nuna ba sani ba sabo hatta ga kawayen cinikayyar Amurkan wajen kara musu haraji, kalaman Barrack Obama na baya-bayan nan na barazana ga kwarin gwiwar da Trump ke da shi.

Cikin kalaman da ya gabatar can a Montana da Florida jihohin da Trump ya ziyarta a ranar Laraba, dama gangamin da ya yi a Georgia, Obama ya nemi al’ummar su fito su kada kuri’a dn kawo karshen yiwa dokokin kasarsu karan tsaye.

A cewar Obama Amurka tamkar tudun mun tsira ce ga al’ummar duniya ta inda ta ke basu mafaka tare da tallafa musu bai kamata ta zamo wajen wulakanta su ba.

Sai dai kalaman Trump da ke zuwa bayan na Obama ya ce a shirye su ke su kara yawan guraben aiki tare da hana kwarar baki kasar baya ga dakile ayyukan ta’addanci da kuma kashe kudin kasar ta inda basu da ce ba.

Shi ma dai cikin kalamansa Barrack Obama, ya kafa misali da umarnin gwamnatin Amurkan na harbin ‘yan ciranin Caravan, wadanda ya ce suna kan hanyar su ne saboda sun yi imani da Amurka.

Ka zalika ya gwada misali da shirin gwamnatin na soke damar zama Ba’amurke ga duk dan da aka haifa can, matakin da ya ce abin da ya ke roka daga al’umma kadai shi ne su fito su kada kuri’unsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.