Amurka

Amurkawa na kada kuri'a a zaben tsakiyar wa'adi

Ana saran dimbin Amurkawa sun fito don jefa kuri'unsu
Ana saran dimbin Amurkawa sun fito don jefa kuri'unsu REUTERS/Aaron Josefczyk

Al’ummar Amurka na kada kuri’a a wannan Talata a zeben tsakiyar wa’adi da zai fayyace makomar rinjayen jam’iyyar Republican mai mulki a Majalisar Dokokin Kasar.

Talla

Republican da babbar mai hamayya da ita, wato Democrat sun gudanar da zazzafen yakin neman zabe gabanin ranar kada kuri’ar, in da kowanne bangare ke bayyana kwarin gwiwar samun nasara.

Kuri’un jin ra’ayoyin jama’a sun nuna cewa, jam’iyyar adawa ta Democrat za ta samu gagarumar nasara a Majalisar Wakilai, yayin da Republican ta shugaba Donald Trump za ta ci gaba da rinjaye a Majalisar Dattijai.

Jam’iyyun biyu na fafutukar lashe kujeru 435 a Majalisar Wakilai da kuma 36 daga cikin 100 a Majalisar Dattawa. Kazalika za a gudanar da zaben gwamnoni a jihohi 36 daga cikin 50.

Shugaba Trump ya dukufa wajen zagaye sassan Amurka da sunan yakin neman zabe, in da a ranar Litinin kadai ya ziyarci jihohi uku.

Sai dai shugaban a yayin ziyarsa a jihar Indiana ya amsa cewa, akwai yiwuwar jam’iyyarsa ta rasa rinjaye a Majalisar Wakilai.

Ana saran dimbin jama’a su fito don kada kuri’arsu a zaben na yau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.