Mu Zagaya Duniya

Shugabannin kasashe na taron bikin cika shekaru 100 da kawo karshen yakin duniya na 1

Sauti 20:02
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, yayin karrama iyalan tsaffin sojin kasar da suka mutu a yakin duniya na 1.
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, yayin karrama iyalan tsaffin sojin kasar da suka mutu a yakin duniya na 1. © Ludovic Marin/Pool via REUTERS

Shirin Mu Zagaya Duniya ya yi waiwaye wanda masu iya magana suke cewa adon tafiya, kan wasu daga cikin muhimman al'amuran da suka faru cikin makon da ya kare, a sassan duniya. Daga cikin wadannan muhimman al'amura akwai taron da shugabannin kasashen duniya ke halarta na bikin cika shekaru 100 da kawo karshen yakin duniya a birnin Paris, wanda gwamnatin shugaba Emmanuel Macron ta joranci shiryawa.