Isa ga babban shafi
Najeriya-Faransa

Masu cin rashawa ba sa tsoron gidan yari- Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a yayin taron zaman lafiya a birnin Paris na Faransa
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a yayin taron zaman lafiya a birnin Paris na Faransa RFI
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad | Bashir Ibrahim Idris
Minti 2

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewar matsalar cin hanci da rashawa da halarta kudaden haramun sun yi girma a kasar ta yadda wadanda zuciyarsu ta zarme da aikata irin wannan laifi ba sa tsoron zuwa gidan yari.

Talla

Yayin gabatar da jawabinsa wajen taron zaman lafiyar da ya gudana a birnin Paris da ke Faransa, Buhari ya bukaci kasashen duniya su hada kai wajen mayar wa kasashe kudadensu da aka sace da ribar kudin da aka samu wajen ajiyarsu a bankuna.

Shugaban Najeriyar ya bayyana kalubalen da ke fuskantar kasashe masu tasowa da suka hada da sace dukiyar gwamnati da rage kudaden shiga da harajin da ake yi wa jama’a aiki da karancin masu zuba jari saboda rashin yarda da shugabanni da kuma kyakyawar tsarin da zai bai wa masu zuba jari kwarin gwiwar shigar da kudadensu.

Buhari ya ce, sace kudaden gwamnati ana kai su wasu kasashe domin boyewa, na hana ‘yan kasa amfana da dukiyarsu, yayin da manyan kasashen duniya da wasu hukumomin ke taimakawa masu aikata irin wannan laifin wajen boye dukiyar ta sata sakamakon wasu dokoki masu sarkakiya da ake da su.

Shugaban ya kare matakan da gwamnatinsa ke dauka na yaki da cin hanci da rashawa wanda ya ce ana gudanar da su ne kamar yadda dokokin kasa suka tanada.

Buhari ya ce, shirin da gwamnatinsa ta bullo da shi na bada tukuici ga duk wanda ya tona asirin masu satar kudin gwamnatin ya taimaka wajen gano tarin dukiyar da aka sace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.