Mutane 149 sun hallaka cikin sa'o'i 24 a Yemen

Dakarun gwamnatin Yeman na taruwa kusa da birinin Hodeida domin kwace birnin daga hannun 'yan tawaye
Dakarun gwamnatin Yeman na taruwa kusa da birinin Hodeida domin kwace birnin daga hannun 'yan tawaye STRINGER / AFP

Mutane akalla 149 suka mutu a kazamin fadan da ke gudana tsakanin dakarun gwamnatin Yemen da 'Yan Tawayen Houthi a garin Hodeida.

Talla

Majiyar asibiti da sojin kasar, sun ce a cikin sa’oi 24 an kashe Yan Tawaye akalla 110, yayin da mayakan gwamnati 32 suka rasa rayukan su.

Rahotanni sun ce kokarin karbe iko da birnin Hodeida mai tashar jiragen ruwa ya gamu da tirjiya sosai daga 'Yan Tawayen dake iko da shi.

Fafatawar tsakanin mayakan Houthi da ke samun goyan bayan kasar Iran da na dakarun gwamnati da Saudiya ke marawa baya, ta kaiga kutsawa unguwannin da gidajen jama suke.

Rahotanni sun ce dakarun gwamnati sun kutsa kai cikin titunan birnin inda suke farautar 'Yan Tawayen dake dauke da makami, domin kakkabe su.

Ya zuwa yanzu an kashe akalla mayaka 400 a cikin kwanaki 10 da aka kwashe ana gwabzawa a birnin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.