Amurka

Alkaluman mamata a California sun karu

Wutar dajin California ta lakume rayukan jama'a da dama
Wutar dajin California ta lakume rayukan jama'a da dama REUTERS/Eric Thayer TPX IMAGES OF THE DAY

Adadin wadanda suka mutu sakamakon wutar dajin da ke ci gaba da ruruwa a jihar California da ke Amurka sun kai 42 a halin yanzu.

Talla

An samu karin sabbin gawarwaki 13 a garin Paradise da wutar da dajin ta yi wa  illa sosai a yankin arewacin jihar ta California.

Akalla mutane 228 sun bace yayin da wutar dajin ta cinye kusan gine-gine dubu 7 da 200, in da kuma kimanin dubu 15 da 500 ke cikin barzanar konewa.

Jami’an agaji sun ce sama da mutane dubu 300 ne aka kwashe daga yankin da wannan gobara ta shafa.

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana ibltila’in a matsayin gagarumi tare da tanadin agajin gwamnatin tarayya ga wadanda lamarin ya shafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.