Korea ta Arewa

Koriya ta Arewa ta jagoranci bikin kaddamar da wasu sabbin makaman yaki

Kim Jong Shugaban Korea ta Arewa
Kim Jong Shugaban Korea ta Arewa KCNA/via REUTERS

A yau juma’a shugaban Koriya ta Arewa ya jagoranci bikin kaddamar da wasu sabbin makaman yaki da ake ganin cewa zai sa a diga ayar tambaya dangane da shirin kasar na kwance wa kanta damarar nukiliya.

Talla

A yan watanni da suka gabata a lokacin shiga tattaunawa da Koriya ta kudu da Amurka ma’aikatar leken asirin kasar Amurka ta bayyana matukar damuwarta, inda ta ce yanzu haka kasar Koriya ta arewa na ci gaba da kera wasu sabbin makamai masu linzame dake cin zangon kasa da kasa

Ba sabon abu bane kasar Koriyar ta arewa ta furta cewa, tana iya kera makaman da zai iya cin dogon zangon da zai kai ga kasar Amruka

Kamfanin dillancin labaran kasar ya ce Shugaba Kim Jong Un da kansa ya halarci bikin kaddamar da wadannan makamai da aka yi a sanyin safiyar yau jumaa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.