Faransa

Ana Babban Zanga-Zanga a Fadin Faransa

Hotunan wasu daga cikin masu zanga-zanga a Faransa
Hotunan wasu daga cikin masu zanga-zanga a Faransa rfi

Dubban matuka ababan hawa a fadin kasar Faransa suka shiga zanga-zangan da aka kira yau Asabar karkashin kungiyar masu sanye da riguna masu ruwan kwai “Yellow Vest” saboda nuna adawa da tsadar  Mai na ababan hawa a kasar.

Talla

Mutane kusan dubu 500 suka shiga zanga-zangan na yau a wurare dubu daya a sassan kasar kamar yadda Ministan harkokin cikin gida Christophe Castaner ya sanar.

Wasu bayanai na nuna an sami rasa rai na wata mace dake kan hanyar kai ‘yarta asibiti a lokacin da masu bore suka kewaye motar ta aka rika dukan motar.

Masu zanga-zangan na adawa ne da matakan da shugaban kasar Emmanuel Macron ke dauka na rage gurbacewar yanayi dake haifar da tsadan man fetur .

Ministan ya bayyana cewa ana daukan matakai don tabbatar da ba’a sami mummunar yamutsi ba ko rufe hanyoyi da zai iya kai ga rudani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.