Amurka-California

Mutanen da wutar dajin California ta hallaka sun tasamma 80

Ko a ziyarar da Trump ya kai jihar ta California a karshen mako ya bayyana wutar da mafi muni a tarihin jihar.
Ko a ziyarar da Trump ya kai jihar ta California a karshen mako ya bayyana wutar da mafi muni a tarihin jihar. Reuters

Adadin mamata sakamakon wutar daji da ke cigbaa da ruruwa tsawon kwanaki 11 a jihar California da ke Amurka sun kai 77 a halin yanzu.

Talla

Shugaban rundunar ‘yan sanda a gundumar Butte da ke arewacin California ya ce daga cikin mutane 77 da suka hallaka, an tantance 67, yayin da dubban gidaje suka kone kurmus.

Ana dai ganin wannan gobara ita ce mafi muni da birnin na California ke fuskanta musamman ta fuskar saurin fantsamuwa tare da kone gidaje.

A makon da ya gabata ma shugaban kasar Donald Trump ya kai ziyarar jaje ga al'ummar yankin inda ya bayyana ta mafi lakume dukiya baya ga tarin rayukan da aka yi asara.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.