Australia

An fara amfani da jirgin fasinja wajen kashe wutar dajin Australia

Tuni dai jirgin ya taka muhimmiyar rawa wajen kashe wutar da ke kokarin kone gidajen da ke Port Stehens mai nisan kilomita 150 da arewacin Sydney.
Tuni dai jirgin ya taka muhimmiyar rawa wajen kashe wutar da ke kokarin kone gidajen da ke Port Stehens mai nisan kilomita 150 da arewacin Sydney. Reuters

An fara amfani da jirgin Fasinja wajen kai dauki don kashe wutar dajin jihar new south wales ta Australia yau Juma’a wanda kuma shi ne karon farko da aka taba gani a tarihin kai daukin kashe wuta a duniya.

Talla

Jirgin kirar Boeing 737 wanda hukumomi suka sahale masa aikin kai daukin kashe wutar tun a jiya Alhamis yana daukar fiye da litar ruwa dubu goma sha biyar a duk jigila daya baya ga tarin ma’aikatan kashe gobara akalla 63 da ke aikin watsa ruwan.

Tuni dai jirgin ya taka muhimmiyar rawa wajen kashe wutar da ke kokarin kone gidajen da ke Port Stehens mai nisan kilomita 150 da arewacin Sydney.

Rahotanni sun ce wutar wadda yanzu haka ta cinye wuri mai fadin kadada dubu daya da dari biyar, a yau juma’a ta fara lafawa bayan daukar matakin fara kai agaji da jirgin na 737 tare kuma da taimakon wasu kananan jiragen kashe gobara 9.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.