Iran-Saudiya

Rouhani ya bukaci hadin kan Iran da Saudiya don kalubalantar Amurka

Yayin wani taron hadin kan kasashen Musulmi Hassan Rouhani ya ce dole ne sai kasashen su juyawa Amurka baya, ta haka ne za su tsira da mutuncinsu tare da kaucewa makircinta.
Yayin wani taron hadin kan kasashen Musulmi Hassan Rouhani ya ce dole ne sai kasashen su juyawa Amurka baya, ta haka ne za su tsira da mutuncinsu tare da kaucewa makircinta. ایرنا

Shugaban Iran Hassan Rouhani ya yi kira ga Musulmin duniya da su hada kan su wajen yaki da manufofin Amurka, yayin da ya shaidawa Saudi Arabia cewar kar ta ji tsoron komai dangane da ita.

Talla

Yayin jawabi ga wani taron hadin kan addinin Islama a Tehran, Rouhani ya ce bukatar Amurka ita ce mayar da Gabas ta Tsakiya bayi, saboda haka ya zama wajibi ga kasashen Musulmi su hada kan su domin fuskantar ta.

Shugaban ya bukaci Saudi Arabia da ta kawo karshen dogaro da agajin sojin da ta ke samu daga Amurka, inda ya ke cewa a shirye Iran ta ke ta kare Saudiya da muradun ta daga duk wani harin ta’addanci da kuma kasashe masu karfi.

Rouhani ya ce ba za su bukaci a biya su Dala biliyan 450 domin kare Saudiya ba, kuma ba za su ci mutuncin kasar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.