Amurka-Mexico

Jami'an tsaron Amurka sun azabtar da 'yan ci ranin kan iyakar Mexico

Jami'an tsaron sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da kuma harsashin roba wajen tarwatsa 'yan ciranin wadanda ke kokarin danno kai kasar ta Amurka.
Jami'an tsaron sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da kuma harsashin roba wajen tarwatsa 'yan ciranin wadanda ke kokarin danno kai kasar ta Amurka. ©REUTERS/Ueslei Marcelino

Jami’an tsaron Amurka sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye tare da harsashin roba kan dandazon ‘yan cirani 5000 da ke kan iyakar kasar da Mexico a wani mataki na hana su shigowa cikin kasar bayan umarnin Donald Trump da ke nuna cewa sai sun samu izini shiga kasar za su bar kan iyakar.Tuni dai jami’an suka sanar da kame mutane 42 da suka yi taurin kan tsallakowa Amurkan.

Talla

A cewar jami’an da ke kula da kan iyakar ta Tijuana dandazon ‘yan gudun hijirar su 5000 na kokarin bijirewa umarnin da aka ba su na ci gaba da kasancewa a Mexico har zuwa lokacin da za a basu izinin shiga Amurka, dalili kenan da ya sa aka yi amfani da hayakin mai sanya hawaye baya ga harsashin roba don tilasta musu komawa cikin kasar Mexico.

Hukumar kula da shige da fice ta Amurka da ke San Diego a birnin California ta sanar da kulle kan iyakar ta wasu ‘yan sa’o’I bayan artabun tsakanin dandazon ‘yan gudun hijirar wadanda galibi suka fito daga Honduras da kuma jami’an tsaron na Amurka.

Rufe kan iyakar na ‘yan sa’o’I na zuwa kwanaki 3 bayan Donald Trump ya yi barazanar kulle iyakar baki daya matukar Mexico ta ci gaba da bai ‘yan gudun hijira damar tsallakowa Amurka wanda ya yi ikirarin cewa Amurkan ba za ta iya kula da suba.

A cewar ministan harkokin cikin gida na Mexico Alfonso Navarrete wasu daga cikin ‘yan ci ranin sun yi kokarin tsallake iyaka wajen shiga Amurka ta kowanne hali, wanda ya ce tabbas sun saba ka’ida amma kamata ya yi jami’an su taimaka musu ta hanyar mayar da su salin-alin maimakon harbinsu da harsashin roba baya ga bule su da barkonon tsohuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.