G20: Kungiyar BRICS ta soki kasashen da ke fifita bukatunsu

Shugabannin kasashen kungiyar G20 dake taro a Buenos Aires, babban birnin Argentina. 30/11/2018.
Shugabannin kasashen kungiyar G20 dake taro a Buenos Aires, babban birnin Argentina. 30/11/2018. REUTERS/Marcos Brindicci

Kasashen kungiyar BRICS mafiya samun bunkasar tattalin arziki a duniya, sun yi Alla-Wadai da tsari ko manufar fifta bukatun kai dake karuwa musamman ta fannin tattalin arziki tsakanin kasashe.

Talla

Kasashen na BRICS da suka hada da China, India Rasha, Brazil, da Afrika ta Kudu, sun yi bayyana haka ne yayin gudanar da taron kungiyar kasashen G20 mafiya karfin tattalin arziki a duniya, wanda kasar Argentina ke karbar bakunci.

Yayinda aka shiga rana ta biyu na taron G20n hankula za su koma kan ganawar da ake sa ran za’a yi tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da kuma takwaransa na China Xi Jinping.

Idan za’a iya tunawa da, ana gaf da soma wannan taron kungiyar na G20 ne, shugaba Trump ya ce zai kara fadada harajin dala biliyan 200 da ya kakabawa kayan da China ke shigarwa Amurka.

A halin da ake ciki dai da dama musamman tsakanin masu sharhi kan alakar shugabannin biyu basu da kwarin cewar za’a cimma kwakkwarar yarjejeniya a tsakanin bangarorin biyu, domin kawo karshen yakin kasuwancin da ya barke tsakanin Amurkan da China.

Idan za’a iya tunawa, ana gaf da soma wannan taron kungiyar na G20 ne, shugaba Trump ya ce zai kara fadada harajin dala biliyan 200 da ya kakabawa kayan da China ke shigarwa Amurka.

Zalika shugaban na Amurka ya koma bayyana cewa zai sake kakabawa harajin dala biliyan 267 akan wasu kayayyakin na dabam da kasar ta China ke shigarwa kasarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI