Alhaji Umaru Dembo kan matakin Qatar na ficewa daga kungiyar kasashe masu arzikin man fetur OPEC

Sauti 04:04
Saad al-Kaabi, ministan albarkatun man fetur na Qatar.
Saad al-Kaabi, ministan albarkatun man fetur na Qatar. Naseem Zeitoon/ REUTERS

Kasar Qatar ta sanar da ficewar ta daga kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta duniya, OPEC, domin mayar da hankalin ta kan kasashe masu arzikin gas.Ministan makamashin kasar, Saad al-Kaabi ya bayyana haka a wani taron manema labarai kuma yace tuni suka mikwa kungiyar takardar su. Dangane da wannan mataki, mun tattauna da Alhaji Umaru Dembo, tsohon ministan albarkatun man Najeriya, kuma ga tsokacin da ya yi akai.