Yemen

Tattaunawar kawo karshen rikicin Yemen

Martin Griffiths mai shiga tsakanin rikicin Yemen cikin shirin barin kasar
Martin Griffiths mai shiga tsakanin rikicin Yemen cikin shirin barin kasar REUTERS/Mohamed al-Sayaghi

Wakilan yan Tawayen Huthi yanzu haka suna kasar Sweden domin shiga tattaunawar Majalisar Dinkin Duniya don ganin an kawo karshen rikicin da aka kwashe shekaru 4 ana fafatawa wanda yayi sanadiyar hallaka daruruwan rayuka cikin su harda da tsohon shugaban kasa Ali Abdallaha Saleh.

Talla

Jakadan Majalisar Martin Griffiths ya kwashi tawagar yan tawayen daga Birnin Sana’a zuwa Sweden, kwana guda bayan an kwashe yan tawaye 50 da suka samu raunuka zuwa Oman domin samun magani.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane miliyan 14 ke fuskantar azabar yunwa yanzu haka a kasar.

Idan aka yi tuni Sakataren tsaron Amurka, Jim Mattis ya ce a baya, Saudiya da Hadaddiyar Daular Larabawa da ke goyon bayan shugaba Abd-Rabbu Mansour Hadi a mummunan rikicin tsawon shekaru uku, sun shirya halartar zaman sulhun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.