Taron sasanta rikicin Yemen ya kankama a Sweden
Wallafawa ranar:
Yau alhamis aka fara tattaunawar sulhu tsakanin wakilan gwamnatin Yemen da kuma ‘yan tawayen Huthi, karkashin inuwar Majalisar Dinkin Duniya, taron da ke gudana a kusa da birnin Stockholm na kasar Sweden.
Yemen, kasar da ta fi kowace talauci a tsakanin kasashen Larabawa, ta tsunduma a cikin mummunan yakin basasa ne tun a shekarar 2014, inda dakarun gwamnati da ke samun goyon bayan wata gagarumar rundunar kawancen kasashen duniya karkashin jagorancin Saudiyya ke gwabza fada da mayakan kungiyar da ake kira Huthi masu samun goyon bayan kasar Iran.
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana tattaunawar da aka fara a wannan alhamis a matsayin wata dama don kawo karshen wannan yaki da ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mutane dubu 10, yayin da mutane milyan 14 ke fama da matsananciyar yunwa.
Manzon musamman da Majalisar Dinkin Duniya ta dora wa alhakin sulhunta wannan rikici Martin Griffiths dan kasar Birtaniya, shi ne ke jagorantar wannan tattaunawa da ke gudana a wani karamin gari mai suna Rimbo, mai tazarar kilomita 50 daga birnin Stockholm.
Griffiths ya ce ba ya da tabbas idan har za a cimma jituwa a lokacin wannan tattaunawa, to amma ko shakka babu lura da yadda aka fara ta akwai alamun da ke dada kwarin gwiwar cewa za a samu gagarumin cigaba a yunkurin kawo karshen wannan yaki na kasar Yemen.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu