Afrika-Majalisar Dinkin Duniya

Trump ya kalubalanci karfafa rundunar samar da zaman lafiya

Yanzu haka Amurkan ta gindaya sharudda 11 wadanda ta ce sai jakadun Afrikan sun amince da su gabanin kada kuri’ar amincewa da kudirin.
Yanzu haka Amurkan ta gindaya sharudda 11 wadanda ta ce sai jakadun Afrikan sun amince da su gabanin kada kuri’ar amincewa da kudirin. REUTERS/Emmanuel Braun

Shirin kasashen Afrika na tabbatar da tallafin Majalisar Dinkin Duniya ga dakarun musamman da ke wanzar da zaman lafiya a Nahiyar na fuskantar kakkausar suka daga Amurka bayan da ta gindaya sharuddan da ke nuna cewa sai kasashen sun amince da su kafin da bada damar tabbatuwar kudurin.

Talla

Cikin sharuddan da Amurka ta gindaya gaban zaman majalisar dinkin duniyar, ta ce matukar ana bukatar amincewarta da shirin na tallafawa rundunonin da kudaden da za su iya magance rikice-rikicen da yankin ke fuskanta, sai dai in har kasashen da kan su za su samar da kashi 25 cikin dari na adadin kudaden tallafin da su ke bukata.

Kudurin wanda kasashen Afrika 3 mambobi a kwamitin tsaron na Majalisar Dinkin Duniya suka shigar da suka hadar da Ethiopia, Equtorial Guinee da kuma Ivory Coast na samun goyon bayan kasashen Faransa da China wadanda ke ganin ta hakan ne kawai za a magance matsalar nahiyar.

Rahotanni sun ce yanzu haka Amurkan ta gindaya sharudda 11 wadanda ta ce sai jakadun Afrikan sun amince da su gabanin kada kuri’ar amincewa da kudirin na su a mako mai zuwa.

Ana dai ganin amincewa da kudurin zai taimakawa rundunar hadin gwiwa tsakanin kungiyar Tarayyar Afrika da kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin samar da kayakin aiki baya ga karfafa rundunar da tunkarar kalubalen da yankin ke fuskanta a dai dai lokacin da dakarun Afrika ke matsayin rabin rundunar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI