UNICEF-WHO

UNICEF da WHO sun koka kan haifar jarirai miliyan 30 da nakasa

UNICEF, tare da hadin gwiwar hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya WHO a rahoton da suka gabatar bayan gudanar da binciken sun koka matuka da halin da jariran kan tsinci kan su.
UNICEF, tare da hadin gwiwar hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya WHO a rahoton da suka gabatar bayan gudanar da binciken sun koka matuka da halin da jariran kan tsinci kan su. AFP/Oli SCARFF

Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce kusan jarirai miliyan 30 ake haihuwa tattare da matsalolin da suka kunshi, kakanta fiye da kima, cutukan da ke salwantar da rayukansu ko kuma haihuwar jariran a matsayin bakwaini ko kasa da haka.

Talla

UNICEF, tare da hadin gwiwar hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya WHO a rahoton da suka gabatar bayan gudanar da binciken sun koka matuka da halin da jariran kan tsinci kan su.

Mataimakin darakatan UNICEF Omar Abdi ya ce kusan ilahirin miliyoyin jariran da suka ji ciwo a kwakwalwa yayin haihuwarsu, sauran cutukan da suka shafi jiki, ko kuma wadanda aka Haifa a matakin bakwaini, kan rasa ransu ko kuma a wasu lokatan su kare rayuwarsu da nakasa.

Rahoton ya kara da cewa a shekarar 2017, jarirai miliyan 2 da rabi ne suka mutu, mafi akasarinsu kuma sakamakon fama da cutukan da za a iya magancewa, zalika kashi 2 bisa 3 na jariran an haifi su ne a mataki na bakwaini ko kasa da haka.

A cewar rahoton ko da ace jariran sun rayu, akwai hasashen masana lafiya mai karfi da ke nuna cewa za su iya fuskantar cutuka daban daban wadanda ka iya nakasa bunkasar girman jiki da kaifin kwakwalensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI