Saudiya-Amurka

Saudiya ta soki kudirin Majalisar Dattawan Amurka

Kudirin Majalisar Dattawan Amurka ya alakanta Yarima mai Jiran Gado, Mohammed Bin Salman da kisan Jamal Khashoggi a Turkiya
Kudirin Majalisar Dattawan Amurka ya alakanta Yarima mai Jiran Gado, Mohammed Bin Salman da kisan Jamal Khashoggi a Turkiya AFP Photo / Saudi Royal Palace / Bandar al-Jaloud

Saudiyya ta mayar da zazzafan martani game da kudurin da Majalisar Dattawan Amurka ta dauka da ke sukar rawar da kasar ke takawa a rikicin kasar Yemen tare da danganta Yarima Mohammed bin Salman da kisan dan jarida Jamal Khashoggi.

Talla

Saudiyyan ta bayyana zargin na ‘yan Majalisar Dattawan Amurkan a matsayin mara hujja, tare da bayyana Majalisar a matsayin wadda ta yi shisshigi a lamurran cikin gidan kasar, abin da kuma zai iya gurgunta alakar da ke tsakanin kasashen biyu.

A ranar Alhamis da ta gabata ne Majalisar wadda ke karkashin rinjayen Jam’iyyar
Republican, ta kada kuri’ar kawo karshen agajin soji da Amurka ke bai wa Saudiya a yakin da take jagoranta a Yemen.

Ana kallon wannan kuiri’ar a matsayin gagarumin koma-baya ga shugaba Donald Trump wanda ke nuna goyon baya ga gwamnatin Saudiya a dai dai lokacin da take shan matsin lamba daga kasashen duniya musamman saboda kashe Jamal Khashoggi a Turkiya.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Mike Pompeo ya kare zumuncin da ke tsakanin kasashen biyu ta fuskar wanzar da tsaro , in da yake cewa, Saudiya ce bangon da ke dakile babbar makiyiyarsu wato Iran.

Manazarta sun ce, mawuyaci ne, kudirin da Majalisar ta Amurka ta kada ya zama doka duk da cewa batun ya dauki hankali matuka, amma babu shakka, hakan ya tona abin da ke cikin zukatan ‘yan Majalisar na rashin amincewa da wasu manufofin Saudiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.