Amurka

Ayyukan gwamnati sun tsaya a Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump Reuters

Matakin dakatar da wasu ayyukan gwamnatin Amurka ya fara aiki bayan ‘Yan Majalisar Dokokin Kasar sun ki amincewa da bukatar shugaba Donald Trump ta ba shi Dala biliyan 5.7 don gina katafariyar katanga akan iyakar kasar da Mexico.

Talla

Ana saran majalisun kasar biyu su lalubo bakin zaren warware wannan takaddama.

Rahotanni na cewa, kashi 1 bisa 4 na ayyukan ma’aikatun gwamnatin kasar sun tsaya sakamakon matakin gwamnati na kin ba su kudade har sai majalisar dattawa ta amince da bukatar ta Trump.

Matakin dakatar da ayyukan zai shafi akalla ma’aikatan gwamnati dubu 800 da za su yi aiki amma ba tare da biyan su ko sisi ba.

Shugaba Trump na bukatar majalisar da ta amince da kudin a kasafin kudin kasar kafin ya rattaba hannu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI