Amurka

Jakadan Amurka a yaki da ISIS ya yi murabus

Brett McGurk
Brett McGurk Reuters/Stephanie McGehee

Jakadan Amurka na musamman a rundunar hadaka ta kasashen da ke yaki da ISIS, Brett McGurk, ya ajiye aikinsa sakamakon matakin shugaba Donald Trump na shirin janye dakarun kasar daga Syria.

Talla

Gabanin Trump ya sanar da aniyar tasa, Mr. McGurk ya jaddada cewa, Amurka za ta ci gaba da aikin kakkabe Kungiyar ISIS da ke tayar da kayar baya a Syria.

Mr. McGurk kwararren jakada ne kuma tsohuwar gwamnatin Barack Obama ne ta nada shi a matsayin wakilinta a yaki da ‘yan ta’adda a Syria.

A ranar Alhamis da ta gabata ne, Sakataren Tsaron Amurkar, Jim Mattis shi ma ya yi murabus bayan ya nuna adawa da matakin Trump na janye dakarun kimanin dubu 2.

Shugaba Trump ya hakikance cewa, an ci galaban mayakan ISIS, don haka lokaci ya yi da ya kamata dakarunsu su koma gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI