Syria-Turkiyya-Amurka

Erdogan ya sha alwashin kakkabe mayakan IS a Syria bayan fitar Amurka

A cewar Erdogan ba za su zuba ido su na kallon 'yan uwansu Larabawa na shan wahala a Syria ba, dole ne su agaza musu.
A cewar Erdogan ba za su zuba ido su na kallon 'yan uwansu Larabawa na shan wahala a Syria ba, dole ne su agaza musu. REUTERS/Umit Bektas

Shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan ya sake aike wasu tarin dakarunsa kan iyakar kasar da Syria a wani mataki da cika alkawarin da ya dauka na kakkabe sauran mayakan IS da na Kurdawa masu barazana ga tsaron kasar.

Talla

Cikin jawaban da ya gabatar, bayan aikewa da dakarun Erdogan ya ce Turkiyya za ta tabbatar da tsaron ‘yan uwansu mata da maza, yara da kanana wadanda ayyukan ta’addancin IS da na ‘yan tawayen Kurdawa suka jefa cikin matsala.

A cewarsa baza su taba juya baya ga ‘yan uwansu larabawan Syria ba, musamman a halin da su ke ciki na bukatar agajinsu.

Matakin na Erdogan na zuwa bayan janye dakarun sojin Amurka masu yaki a Syrian, wanda Donald Trump ya ce ya yi hakan ne bayan cimma matsaya da Erdogan wanda ya sha alwashin yakar mayakan na IS shi kadai.

Tun a daren jiya Laraba wayewar yau Litinin ne jerin gwanon motocin sojin Turkiyya suka shiga Syrian don ci gaba da fatattakar mayakan na IS da ‘yan tawayen kurdawa.

Shugaba Erdogan dai na kallon mayakan na Kurdawa da a baya ke samun goyon bayan Amurka a matsayin 'yan ta'adda wadanda ya ke zargi da haddasa barazanar tsaro ga Turkiyya tun a shekarar 1984.

A cewar shugaban na Turkiyya kwanaki kadan daga yanzu Turkiyya za ta kaddamar da yakin murkushe sauran burbushin na Kurdawa, amma yanzu za ta faro ne daga kan mayakan IS.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI