mexico

Gwamna da mijinta sun mutu a hatsarin jirgi

Gwamnar Jihar Puebla da ke Mexico da mijinta, wanda dan majalisar dattawa ne, sun rasa rayukansu sakamakon hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu kamar yadda shugaban kasar ya sanar.

Gwamna Martha Erika Alonso da mijinta da suka mutu a hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a Mexico
Gwamna Martha Erika Alonso da mijinta da suka mutu a hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a Mexico newsjar.co.uk
Talla

A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Twitter, shugaba Andres Manuel Lopez Obrador ya aika da sakon ta’aziya ga iyalan Sanata Rafael Moreno Valle da uwarginda, Gwamna Martha Erika Alonso.

A ranar 14 ga watan Disamban da muke ciki aka rantsar da Alonso bayan kotun sasanta rikicin zabe ta gamsu da ta nasarar da marigayiyar ta samu a zaben da aka gudanar a cikin watan Yuli.

Yanzu haka Majalisar Dokoki za ta nada Gwamnan rikon kwarya kafin a sake gudanar da wani zaben nan da watanni uku zuwa biyar kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

Shugaban kasar ya ce, za a gudanar da bincike don gano musabbabin aukuwar hatsarin, kuma za a sanar da gaskiyar abin da ya faru a cewarsa.

Kafafen yada labarai na cikin gida sun rawaito cewa, matukin jirgin da kuma wani fasinja guda, su ma sun rasa rayukansu a hatsarin wanda ya auku a gunzumar Santa Maria Coronango da ke jihar Puebla.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI