Amurka

Trump ya ziyarci dakarun Amurka da ke yaki a Iraqi

Shugaba Donald Trump da Uwargidansa a yayin ziyartar sojin Amurka a Iraqi
Shugaba Donald Trump da Uwargidansa a yayin ziyartar sojin Amurka a Iraqi REUTERS/Jonathan Ernst

Shugaban Amurka Donald Trump da uwargidansa, Melania sun kai wa dakarun kasar ziyarar ba-zata a Iraqi don jinjina wa bajintarsu da nasarorin da suka samu a kasar.

Talla

A yayin ziyarar ta Kirismati, shugaba Trump ya ce, Amurka ba ta da aniyar janye dakarunta daga Iraqi.

Ziyarar na zuwa ne bayan kwanaki kalilan da Sakataren Tsaron Amurka, Jim Mattis ya ajiye aikinsa saboda yadda aka samu rarrabuwar kawuna kan tsare-tasaren kasar a yankin Gabas ta Tsakiya mai fama da rikici.

Shugaba Trump ya janye dakarun Amurka daga Syria bayan ikirarin cewa, sun murkushe mayakan ISIS, matakin da ya janyo masa caccaka daga ciki da wajen kasar.

Har yanzu akwai dakarun Amurka dubu 5 da ke cikin Iraqi domin ci gaba taimakwa gwamnatin kasar a yaki da tsirarun mayakan ISIS.

A karon farko kenan da shugaba Trump ke kai ziyara a yankin tun bayan darewarsa kan karagar mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.