Amurka-Mexico

Ma'aikatun gwamnati za su ci gaba da kasancewa a rufe - Trump

Donald Trump ya ce za a dauki duk lokacin da majalisar ke bukata wajen ganin ma’aikatun a kulle muddun ba ta amince da ware dala biliyan biyar wajen gidan katangar ba.
Donald Trump ya ce za a dauki duk lokacin da majalisar ke bukata wajen ganin ma’aikatun a kulle muddun ba ta amince da ware dala biliyan biyar wajen gidan katangar ba. REUTERS/Yuri Gripas/File Photo

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi gargadin cewa ma’aikatun kasar za su ci gaba da kasancewa a kulle yayinda ayyukan gwamnati za su tsaya cak na lokaci mai tsawo bayan gaza cimma matsaya tsakaninsa da ‘Yan majalisun bangaren adawa da kuma na Republican kan makudan kudaden da ya ke bukata don gina katanga a kan iyakar kasar da Mexico.

Talla

Bayan ganawarsa da ‘yan majalisun Jam’iyyar Democract da ke karbar ragamar shugabancin majalisar a jiya, Trump ya gaza samun goyon bayan da yake bukata na ware dala biliyan 5 wajen gina katafariyar katangar da za ta raba kan iyakar Amurkan da Mexico, matakin da ya sanya shi sake gargadin cewa ma’aikatun za su ci gaba da kasancewa a kulle har zuwa lokacin da bukatunsa za su biya.

Nancy Pelosi ta jam’iyyar democract da ta hau kujerar shugabancin majalisar wakilan ta Amurka a yau, cikin jawaban da ta gabatar ta ce bisa tsari da kuma alkawuran da jam’iyyarta suka daukarwa al’ummar Amurka za su dauki dukkan matakan da suka dace wajen ganin an bude ma’aikatun kasar.

Sai dai Donald Trump ya ce za a dauki duk lokacin da majalisar ke bukata wajen ganin ma’aikatun a kulle muddun ba ta amince da ware dala biliyan biyar wajen gidan katangar ba, wadda ya ce garkuwa ce ga al’ummar Amurka tsaronsu da ma kasuwancinsu.

A cewar Kevin McCarthy da ke matsayin shugaban marasa rinjaye na sabuwar Majalisar wadda za ta fara aiki a yau, ‘yan majalisun na bangaren Democract da na Republican za su gana da juna a gobe don fitar da matsaya kan bukatar ta Donald Trump.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.