Saudiya-Turkiya

Kotu ta fara shari'ar wadanda ke da hannu a kisan Khashoggi

Saudiya na ci gaba da fuskantar matsin lamba don tabbatar da adalci kan mutanen da ke da hannu a kisan na Jamal Khashoggi.
Saudiya na ci gaba da fuskantar matsin lamba don tabbatar da adalci kan mutanen da ke da hannu a kisan na Jamal Khashoggi. AFP 2018 OZAN KOSE

Kotu a Saudiya ta soma sauraron shari’ar 5 daga cikin mutane 11 da ake zargi da kashe dan jaridar nan Jamal Kashoggi, a ofishin jakadancin Saudiyyan da ke birnin Istanbul na Turkiya a ranar 2 ga watan Oktoban da ya gabata.

Talla

Bayan soma sauraron shari’ar, babban mai gabatar da kara na saudiya ya bukaci kotun da ta yankewa mutanen hukucin kisa, la’akari da girman laifin da suka tafka, wanda ya rage kimar kasar ta Saudiya a idon duniya.

Tun a ranar 2 ga watan Oktoban bara ne wasu da har yanzu ba a kai ga bayyana sunayensu ba suka yiwa Fitaccen dan jaridar Saudiyyan Jamal Khashoggi kisan gilla a Ofishin jakadancin kasar da ke birnin Santambul na Turkiya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.