Amurka-Mexico

Sabbin Majalisun Amurka za su kawo karshen rufe ma'aikatu

Sabuwar shugabar Majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi.
Sabuwar shugabar Majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi. REUTERS/Joshua Roberts

Sabuwar Majalisar Wakilan Amurka ta zartas da wani kudiri a zamanta na yau Juma’a da zai kawo karshen rufe ma’aikatun gwamnati da kasar ke fuskanta sakamakon gaza cimma matsaya kan ware makuden kudaden da za a gina katanga a kan iyakar kasar da Mexico.

Talla

A zaman Majalisar ta 116 karkashin jagorancin Nancy Pelosi ta Jam’iyyar Democract wadda yanzu ta ke da rinjaye a sabon zauren ta amince da kudirin wanda zai tilasta bude ma’aikatun baya ga nuna halin ko’in kula da bukatar shugaba Trump na ware fiye da dala biliyan 5 don gina katangar.

Shugaban na Amurka Donald Trump ko a jiya Alhamis ya yi barazanar kin amincewa da duk wani yunkurin cirewa kowacce ma’aikata kudaden gudanarwa da Majalisun kasar za su yi har nan da watan Fabarairu face sun amince da ware masa kudin ginin Katangar.

A bangare guda itama Mexico ta kara nanata cewa a shirye ta ke su yi ayyukan ci gaban kasashe tsakaninta da Amurka amma batun bayar da kudin ginin Katanga ta na kallonshi ne tamkar tatsuniya.

Nancy Pelosi wadda ta bayyana matakin ci gaba da kulle ma’aikatun da sassan gwamnatin, ta ce Majalisar ba za ta amince da bukatar ware kudaden ba, yayinda ta sha alwashin tabbatar da bude ilahirin ma’aikatu.

Cikin wani sabon kudirin doka da majalisun biyu ke kokarin zartaswa kowanne lokaci daga yanzu, Majalisun sun ce babu wani gurbi da zai tabo batun kudaden ginin Katangar, ko da dai ‘yan majalisun jam’iyyar Republican na kokarin bijirewa kudirin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.