AMurka-Syria

Amurka na kokarin kwantar da hankalin Gabas ta Tsakiya

Mashawarcin shugaban Amurka kan harkokin tsaro,  John Bolton
Mashawarcin shugaban Amurka kan harkokin tsaro, John Bolton REUTERS/Maxim Shemetov

Mai bai wa shugaba Trump shawara kan harkokin tsaro John Bolton na ci gaba da ziyara a kasashen yankin gabas ta tsakiya, a wani mataki na kwantar musu da hankali bayan matakin kasar na janye dakarunta daga Syria. Bolton wanda  ya isa Isra’ila a karshen mako, ana saran isarsa Turkiyya a ranar Litinin don ganawa da shugaba Recep Tayyib Erdogan.

Talla

Ziyarar Bolton wadda ke zuwa gabanin makamanciyarta daga sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo da ke shirin ziyarta kasashen yankin 8, na dada kara kwarin gwiwa ga kasashen wajen ganin sun iya kula da kansu game da al’amuran da suka shafi tsaro.

A tattaunawarsa da Benjamin Netanyahu na Isra’ila, Bolton ya nanata bukatar Amurka ta kawo karshen karan-tsayen da Iran ke yi wa tsaron yankin musamman rawar da ta ke takawa a Syria.

Mashawarcin shugaban na Amurka kan harkokin tsaro ya bayyana cewa, ficewar Amurka daga Syria ba hakan na nufin sun fitar da rai daga samar da tsaron kasar ba ne, face tabbatar da ganin an kammala fatattakar sojin Iran daga Syria.

Sai dai yayin tattaunawarsa da Recep Tayyib Erdogan a yau Litinin, kai tsaye za su tattauna rawar da kasashen ke takawa wajen bayar da tsaro ga yankin da kuma kawo karshen yake-yaken da kasashen gabas ta tsakiya ke fuskanta.

A bangare guda, yayin ziyarar Mike Pompeo cikin makon nan a Saudiya da Oman da Iraqi da Masar da Abu Dhabi da Qatar da kuma Kuwait, zai tabo batun karfafa rundunonin sojinsu sabanin dogara da wasu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI