Japan

An yi kuskuren zargi na a Nissan- Ghosn

Carlos Ghosn
Carlos Ghosn REUTERS/Charles Platiau/File Photo

Tsohon shugaban Kamfanin kera motoci na Nissan, Carlos Ghosn ya shaida wa wata kotu a birnin Tokyo na Japan cewa, an yi kuskuren zargin sa da kuma tsare shi kan badakalar cin hanci da rashawa a kamfanin.

Talla

A karon farko kenan da Mr. Ghosn ke bayyana a gaban kotu tun bayan cafke shi a cikin watan Nuwamban da ya gabata bisa zargin sa da wawure kudaden kamfanin motocin na Nissan ba bisa ka’ida ba.

Gohsn da a can baya ake matukar mutuntawa a duniyar kere-keren motoci, ya shiga harabar kotun da hannayensa biyu a cikin ankwa, sannan kuma ga wata igiya rataye a wuyansa.

Iyalan Gohsn mai shekaru 64, sun ce, ya rame sosai a yanzu, in da kilo 20 na kibarsa ya zube sakamakon shinkafar da ake dirka masa a wurin da ake tsare da shi a birnin Tokyo, kana furfura sun fara yi masa yawa a cawarsu.

Sai dai a yayin jin bahasin a kotun, tsohon shugaban na Nissan ya ce, an tafka kuskure wajen zargin sa kuma babu wasu gamsassun hujjoji da ke tabbatar da zargin, yayin da yake cewa, a koda yaushe yana aiki ne da gaskiya.

Har dai aka kammala sauraren bahasin, tsohon babban jami’in bai nuna wata alamar tausayi ba, hasali ma ya bige da kallon wani hoto ne da aka rataye a dakin kotun, yayin da ya yi ta tari jifa-jifa.

A halin yanzu dai, Gohsn zai ci gaba da kasancewa a tsare, amma lauyoyinsa sun ce, za su daukaka kara don ganin an sako shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI