Amurka-Syria

Pompeo ya jaddada matakin Amurka na janye dakarunta a Syria

Mike Pompeo a ziyarar da ya kai Iraqi.
Mike Pompeo a ziyarar da ya kai Iraqi. Andrew Caballero-Reynolds/Pool via REUTERS

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya jaddada alwashin Amurka na janye dakarunta daga kasar Syria. Pompeo ya bayyana haka ne, yayin da ya ke shirin gabatar da jawabi na musamman kan manufofin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya.

Talla

Sakataren harkokin wajen na Amurka ya sake tabbatar da batun janye dakarunsu daga Syria ne yayin taron manema labarai na hadin giwa tare da takwaransa na Masar Sameh Shukry.

Tun a yammacin jiya Laraba Pompeo ya isa birnin Alkahira na Masar, a ci gaba da ziyarar da ya ke a yankin Gabas ta Tsakiya.

Makasudin ziyarar dai shi ne karfafawa kawayen Amurka gwiwa domin dorewar kawancen da ke tsakaninsu na fuskantar barazanar da Iran ke yi wa manufofinsu, da kuma kawo karshen kungiyoyin mayaka ‘yan ta’adda a yankin na Gabas ta Tsakiya, duk da cewa Amurkan za ta janye sojinta daga kasar Syria.

Kafin karasawa Saudiya kowanne lokaci daga yanzu, ana sa ran sakataren harkokin wajen na Amurka Mike Pompeo, ya tabbatar da karfin kawancen da ke tsakaninsu da Saudiya, duk da kisan gillar da aka yi wa dan jaridar kasar Jamal Kashoggi a Turkiya, laifin da ake zargin hannun Yarima mai jiran gadon sarautar Saudiya Muhammad bin Salman.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.