Syria-Amurka

Rukunin farko na sojin Amurka sun fara ficewa daga Syria

Wannan dai ne karon farko da Sojin ke ficewa daga Syrian tun bayan daukar matakin a watan jiya.
Wannan dai ne karon farko da Sojin ke ficewa daga Syrian tun bayan daukar matakin a watan jiya. REUTERS

Rukunin farko na hadakar sojin da ke samun goyon bayan Amurka a Syria sun fara ficewa daga sassan kasar, kasa da wata guda bayan sanarwar da Donald Trump ya yi na janye Ilahirin dakarunsa da ke yaki da IS a kasar.

Talla

Mai magana da yawun hadakar sojin masu samun goyon bayan Amurka Colonel Sean Ryan ya shaidawa AFP cewa wani rukuni na sojin sun fara ficewa daga Syria a yau Juma’a sai dai bai bayyana tsawon lokacin da za a dauka basu kammala ficewar ba.

Tun a shekarar 2014 ne Hadakar Sojin da suka kunshi na Faransa da Birtaniya karkashin jagorancin Amurka ke aikin yaki da mayakan IS a kasar ta Syria sai dai ana ganin ficewarsu ba tare kammala kakkabe mayakan ba zai iya kawo tsaiko ga shirin kasar na yaki da ayyukan ta’addanci.

A cewar hukumar kare hakkin dan adam ta Birtaniya da ke sanya idanu kan rikicin kasar, a jiya Alhamis tarin sojin da ke yankin Hasaken a sansanin Rmeilan sun fice daga sansanin hade da tarin manyan motocin yaki da makamai inda suka rage kasa da soji 150.

Wannan dai ne karon farko da Sojin ke ficewa daga Syrian tun bayan daukar matakin a watan jiya, ko da dai shugaban Amurkan Donald Trump ya tabbatar da cewa Sansanin sojin kasar da ke makotan Syria ciki har da Iraqi za su ci gaba da ayyukan da suka saba.

Yanzu haka dai ya ragewa Turkiyya daukar matakin kammala yakar mayakan na IS da ke Syria da kuma Mayakan Turkawa wanda a baya ke samun goyon bayan Amurka inda Turkiya kuma ke kallonsu a ‘yan ta’adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.