Italiya

Italiya ta kame tsohon madugun 'yan tawaye Cesare Battisti

Cesare Battisti tsohon dan tawayen Kwaminsanci da  Italiya ke nema ruwa a jallo tsawon shekaru.
Cesare Battisti tsohon dan tawayen Kwaminsanci da Italiya ke nema ruwa a jallo tsawon shekaru. REUTERS/Max Rossi

Italiya ta yi nasarar cafke tsohon dan tawayen Kwaminisanci da ta ke nema ruwa a jallo Cesare Battisti wanda ya tsere daga yari bayan zartas masa da hukuncin daurin shekaru bisa kisan wasu mutane hudu a tsakankanin shekarun 1970, inda yanzu haka ya isa birnin Rome bayan taso keyarsa daga Bolivia.

Talla

Cesare Battisti da aka garkame a gidan yari a shekarar 1979 saboda alakarsa da wata haramtacciyar kungiyar juyin yuya hali mai dauke da makamai a Italiya, ya tsere daga gidan kason bayan shafe shekaru biyu a tsare, kuma sama da shekaru 40 kenan da ya arce daga kasar.

Battistis ya isa filin jiragen sama na birnin Rome a yau Litinin, amma babu ankwa a hayyensa, in da ya yi ta yin murmushi a yayin da jami’an tsaro suka tasa shi a gaba.

Ana saran tasa keyar Battistis zuwa gidan yarin Rebibbia, inda zai fara zaman daurin rai da rai kamar dai yadda kafofin yada labaran kasar suka rawaito.

Kasar Italiya ta dauki dogon lokaci tana neman Brazil da ta taso mata keyar tsohon dan tawayen a zaman mulkin Inacio Lula Da Silva, wanda shi ma ke garkame a gidan yari a yanzu.

A ranar asabar da ta gabata ne, aka kama Battisti mai shekaru 64 a birnin Santa Cruz de la Sierra na Bolivia bayan wani samamen hadin guiwa tsakanin jami’an tsaron Italiya da Bolivia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.