Birtaniya

Kasashen duniya sun dauki mataki kan gubar Novichok

Samfurin gubar Novichok da aka yi amfani da shi wajen kai wa Sergei Skripal a Birtaniya
Samfurin gubar Novichok da aka yi amfani da shi wajen kai wa Sergei Skripal a Birtaniya REUTERS/Hannah McKay

Hukumar da ke kula da makamai masu guba ta duniya ta amince da sanya samfurin gubar Novichok da aka yi amfani da ita kan tsohon jami’in leken asirin Rasha da ya koma aiki a Birtaniya, cikin jerin gubar da aka haramta amfani da ita a duniya.

Talla

Kasashen Canada da Netherland da Amurka ne suka shigar da bukatar amincewa da matakin haramta gubar a gaban ilahirin mambobin majalisar kolin hukumar 41 da ke yaki da amfani da makamai masu guba a duniya.

Sabine Nolke babbar jami’ar hukamar ‘yar kasar Canada, ta ce kasashen da ke cikin kungiyar na da wa’adin kwanaki 90 domin su yi nazari tare da amincewa da matakin haramcin kafin ya koma doka a hukumance.

A cewar Jakadan Birtaniya Peter Wilson, matakin babban ci gaba ne a yakin da hukumar ke yi na amfani da makamai masu guba, yayin da shi ma ministan harkokin wajen Netherland ya ce, ta haka ne za a kare dubban rayuka.

An yi ittifakin ita nau’in gubar ta Novichok tarayyar Soviet ce ta samar da ita lokacin yakin cacar baka, kuma kasar da ke da ita a yanzu face Rasha, ko da dai ta musanta hannu a harin wanda aka yi yunkurin kisan Sergei Skripal, tsohon jami’in leken asirin Rashan da ya koma aiki da Birtaniya tare da ‘yar sa Yulia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.