Amurka

IS ta kashe sojojin Amurka a Syria

A karon farko kenan cikin watanni 10 da ake kaddamar da irin wannan harin na kunar bakin wake kan dakarun da Amurka ke jagoranta a yaki da 'yan ta'addan IS a Syria
A karon farko kenan cikin watanni 10 da ake kaddamar da irin wannan harin na kunar bakin wake kan dakarun da Amurka ke jagoranta a yaki da 'yan ta'addan IS a Syria REUTERS/Stringer

Kungiyar IS ta dauki alhakin harin da ya hallaka mutane 15 da suka hada da jami’an sojin Amurka akalla uku a birnin Manbij da ke arewacin Syria, kusa da kan iyaka da Turkiya.

Talla

Kungiyar da ke sa ido kan hakkin bil’adama a Syria, ta ce, fararen hula 9 da kuma dakaru 5 da ke mara wa Amurka baya, na cikin wadanda suka hallaka a harin wanda aka kaddamar kan wani katafaren shagon sayar da abinci.

Kungiyar mai cibiya a Birtaniya ta ce, a karon farko kenan cikin watanni 10 da ake kaddamar da irin wannan farmaki na kunar bakin wake kan dakarun da Amurka ke jagoranta wajen yaki da IS a Syria.

Faifen bidiyon da aka watsa ta kafar dillancin labaran Kurdawa, ya nuna yadda buraguzai suka mamaye wajen shagon sayar da abincin.

Harin na bama-bamai na zuwa ne bayan mayakan Kurdawa da ke da iko da wani yanki mai girma a arewacin Syria, sun ki amince wa da matakin Turkiya na samar da tudun-mun-tsira a kan iyakar kasar.

Turkiya ta dauki tsawon lokaci tana barazanar kai hari kan mayakan Kurdawa da take kallo a matsayin ‘yan ta’adda, yayin da Amurka ta dogara da mayakan na Kurdawa wajen yaki da IS a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.